’Yan bindiga sun sace iyalan Sarkin Hausawa a garin Jere | Aminiya

’Yan bindiga sun sace iyalan Sarkin Hausawa a garin Jere

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Ishaq Isma’il Musa da Abubakar Sadiq Isah

’Yan bindiga sun yi dirar mikiya a gidan Sarkin Hausawa na Unguwar Azara da ke garin Jere a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Mallam Ibrahim Tanko, inda suka sace matansa da ’ya’yansa mata hudu.

A wata hira da ya yi da Aminiya ta wayar tarho, Mallam Tanko ya tabbatar da cewa barayin sun sace matansa biyu; Maimuna Ibrahim and Hauwa’u Ibrahim, amma sun saki Hauwa’u wadda ita ce uwar-gida, bayan da suka ga cewa tana fama da hawan jini.

Ya ce barayin wadanda suka farmaki gidan nasa ranar Talata, da muggan makamai sun je ne da misalin karfe 11:52 na dare.

Ya ce ya yi kokari ne ya gudu inda ya bi ta daya daga cikin kofofin fita na gidan.

Sarkin Hausawan ya kara da cewa bayan da barayin suka bincike gidan ne ba su ganshi ba, sai suka je dakin da ’ya’yansa mata da suke barci suka rutsa su da bindiga suka tafi da hudu daga cikinsu.

Mallam Tanko ya ce ’ya’yan nasa da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su sun hada da; Aisha Ibrahim, Farida Ibrahim, Zainab Ibrahim da kuma Hussaina Ibrahim.

Sannan ya ce bayan da suka bar gidansa ne sai kuma suka shiga na wani makwabcinsa, inda can ma suka tafi da mutum hudu da suka hada da wata mace mai goyo.

Ya ce sun sassari mijin matar da adda, suka barci magashiyan, inda yanzu yana asibiti ana jinyarsa.

Sarkin ya shaida wa wakilinmu cewa bayan sa’a daya da barayin suka tafi da mutanen da suka sata, sai sojoji suka je.

Sai dai yayin da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sanda na Jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige domin tabbatar da ingancin ragoton, ya ce ba su da labarin harin a lokacin.