✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace jami’in Kwastam da wasu mutum 9 a Zariya

Wannan shi ne karo na biyu da suke kai hari gidan jami’in na Kwastam da ke Zariya

’Yan bindiga sun kai hari unguwar Kofar Gayan Low-Cost da ke Zariya a Jihar Kaduna, inda suka sace wani jami’in Kwastam, Mu’awiyya Gambo Turaki da dan shi da kuma wasu mutane.

Maharan dai sun shiga unguwar ne da misalin karfe 9:00 na daren Laraba, sannan suka yi awon gaba da mutanen bayan sun yi harbe-harben razanarwa.

Aminiya ta gano cewa wannan shi ne karo na biyar da ’yan bindigar ke kai hari unguwar, kuma karo na biyu ke nan suna afkawa gidan jami’in, wanda a lokacin azumin bara suka shiga suka dauki matarsa tare da wata mata.

A lokacin dai sai da aka biya kudin fansa Naira miliyan 15 kafin a sako su.

Da yake zantawa da Aminiya, mai anguwar Low-Cost B, Muhammadu Nazifi, ya ce yanzu haka dai ana tsammanin mutum shida ne maharan suka sace, domin guda hudu daga cikinsu sun samu nasarar tserewa.

Ya kara da cewa a cikin wadanda suke hannun ’yan bindigar har da dan shi, mai suna Jamalu, da Muawiyya Gambo Turaki, jami’in Kwastam da kuma dan shi, sai wani mai suna Usman, Jamila da kuma wani yaro Khalifa.

Daya daga cikin wanda ya samu damar kubuta, Yusha’u Isah, ya ce sun samu nasarar ne bisa taimakon Allah, bayan tafiyar kafa ta kimanin kilomita biyar da suka yi.

Ya kara da cewar sun yi amfani da duhun dare ne da kuma ramuka da ke hanyar suka rika mamayar idon maharan suna kaucewa.

Isah, ya ce ’yan bindigar su takwas ne gaba dayansu, amma suna dauke da muggan makamai.

Mafi yawan wanda muka zanta da su sun ta’allaka wannan harin ga masu tsegunta wa ’yan bindigar bayanai, kuma suna ganin kamar maharan sun zo musamman ne saboda su dauki jami’in.

Aminiya ta samu labarin cewa jami’an tsaro sun isa a kan lokaci bayan kiran da aka yi musu, sai dai duk da haka maharan sun riga sun tsere da mutanen da suka sace zuwa cikin daji.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, amma wayar bata shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoto.