✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace karamar yarinya a Katsina

Da tsakar dare suka shiga garin suna harbi kan mai uwa da wabi sannan suka dauke yarinyar

Mahara sun yi garkuwa da wata karamar yarinya mai shekara 12 suka kuma harbi wani mutum a garin Kurfi na Jihar Katsina.

’Yan bindidgar sun shiga garin ranar Lahadi da dare, suna harbi kan mai uwa da wabi kafin su dauke yarinyar wadda mahaifinta ma’akaci ne a Jami’ar Gwamantin Tarayya da ke Dutsinma.

Shugaban ’yan sintirin garin, Nura Liman ya ce misalin 4.00 na asuba ’yan sintirin sun bi sawun maharan, amma suka kasa yin komai saboda ruwan sama da ake yi.

“Mun tare duk hanyoyin shigowa garin muka kuma sa mutanenmu a wuraren da ’yan bindigar za su iya kai hari”, inji shi.

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ba ta kai ga cewa komai game da lamarin ba tukuna.

—Matsalar tsaro a Jihar Katsina

Jihar Katsina ta yi kaurin suna wajen yawaitar hare-haren ’yan bindiga da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Karuwar hare-haren ya sha haddasa zanga-zangar nuna takaici a sassan jihar, wadda daga nan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito.

’Yan jihar a wata zanga-zanga sun bukaci Shugaban Kasar da Gwamna Aminu Masari su sauka daga mukamansu saboda kasa magance matsalar.

Buhari ya sha ba wa manyan hafsoshin tsaro umarnin ganin bayan ’yan bindiga amma har yanzu da sauran rina a kaba.

A watan Yuli Rundunar Sojan Kasa ta Najeriya ta kafa babban sansanin yakar ’yan bindiga a jihar wanda take cewa yana samun nasara.

Sai dai har yanzu ana samun hare-haren ’yan bindiga da ke kashe mutane, su sace wasu da kuma dabbobi tare da yin awon gaba da dukiyoyi da kuma kona gidaje.