✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace makiyaya 10 da shanu 300 a Anambra

’Yan bindigar sun bukaci a biya su miliyan hudu a matsayin kudin fansa.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu makiyaya mambobin kungiyar Miyetti Allah guda 10 tare da sace shanu 300 a Jihar Anambra.

An kai wa Fulanin harin ne cikin dare suna bacci a Obene cikin Karamar Hukumar Ogbaru a Jihar Anambra, a cewar shugaban kungiyar Miyetti Allah shiyar Kudu maso gabashin Najeriya, Alhaji Gidado Siddiki.

’Yan bindigar da aka bayyana sun kai 40 dauke da manyan makamai sun bukaci a biya su miliyan hudu a matsayin kudin fansa da kuma bindiga daga iyalan wadanda aka kama.

Alhaji Gidado Siddiki ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 1.30 na daren ranar Asabar.