✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace malamin coci da wasu mutum 7 a Katsina

An sace su ne da sanyin safiyar Laraba

Wasu ’yan bindiga sun sace wani malamin cocin Katolika da mataimakinsa a kauyen Gidan Mai Kyambu da ke Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina.

An dai sace malamin cocin St. Patrick mai suna Stephen Ojapola Ojapa ne tare da mataimakinsa mai suna Oliver Okpara da sanyin safiyar Laraba.

Wasu majiyoyi a garin Gozaki da Marabar Kanya sun bayyana mana cewa ’yan bindigar sun zo ne kan babura uku, inda suka adana su nesa da cocin, suka kuma karasa wajen a kafa suka sace mutanen.

Kazalika sun ce sun afka wa cocin da duku-dukun ranar Laraba, inda suka sace su da wasu mutane biyu da ake zargin bakin Malamin cocin ne.

Mazauna kauyen Gidan Mai Kanbu sun ce ba su ji karar harbin bindiga ba sai dai motsin tafiyar baburan, kuma sai bayan masu satar mutanen sun tafi ne wadanda ke cikin cocin suka fito waje domin bayyana wa al’umma abinda ya faru.

Cocin Katolika ta Sakkwato dai ta tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ta fitar ta intanet.

A wani labarin mai kama da wannan ma ’yan bindigar ne suka kai hari kauyen Bare-bari da ke Karamar Hukumar Safana a Jihar ta Katsina dai, inda nan ma suka sace mutane.

Wani mazaunin yankin ya ce wani fitaccen dan siyasa mai suna Alhaji Dan Mashbulle na daga cikin wadanda aka sace a harin.

Ya kuma ce ’yan bindigar sun dau lokaci suna bi gida-gida suna satar dabbobi.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, SP Gambo Isa, ya ce ba su da labarin sace mutanen amma za su tuntubi ofishin ’yan sanda da ke Kafur domin jin karin bayani.