✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace manomi a Ekiti

’Yan bindigar sun yi awon gaba da shi yayin da yake tsaka da aiki a gonarsa.

Rundunar ’yan sandan Jihar Ekiti ta bayar da rahoton sace wani manomi a Karamar Hukumar Ikole da ke jihar.

Kakakin ’Yan sandan Jihar, ASP Sunday Abutu ne ya tabbatar da faruwar lamarin yayin ganawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) a Ado-Ekiti, babban birnin Jihar.

  1. Za mu yi maganin ’yan bindiga a Zamfara — Matawalle
  2. Ya mayar da danyar kaza abincinsa

Ya ce, “Tabbas da Yammacin nan wani ya shigar da rahoton sace mutumin a caji ofis din Ikole wanda ya sanar cewa an sace mutumin ne a daren ranar Juma’a.

“Nan da nan muka bai wa jami’anmu cikakken bayanan mutumin kuma suka dukufa don ganin sun ceto shi,” a cewar Abutu.

Bayanai sun ce ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutumin mai suna, Alhaji Jimoh Olodan a lokacin da ya fita noma a wata gonarsa da ke wajen gari.

Wani jagoran al’umma a yankin, Cif Ajayi Ogungbemi, wanda ya tabbatar da faruwar hakan ya ce, ’yan bindigar da adadinsu ya kai 18 sun same mutumin a gona kuma suka tafi da shi ba tare da sun taba wani ba.

Sai dai ya bayyana cewa ’yan bindigar sun rika harbi a iska na tsawon wani lokaci domin razanar da mutane kafin daga bisani su kama gabansu.