✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mata 60 a Zamfara

Maharan sun kashe mutum hudu sun kona gidaje bayan sace mata 60.

Kimanin mata 60 ne aka sace a hare-haren da ’yan bindiga suka kai, inda maharan suka kashe mutum hudu a Jihar Zamfara.

An kai harin ne a ranar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi zaman gaggawa da Majalisar Tsaron Kasa domin tattauna matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.

Dan Majalisar Tarayya, Shehu Ahmed S. Fulani, ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da matan ne bayan mazajensu sun tsere a lokacin harin na kauyen Manawa.

Harin ya kuma yi sanadin mutuwar mutum hudu a kauyukan Randa da Malele, duk a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Dan Majalisar da ke wakilta yankin, ya ce maharan sun kuma kona gidaje masu yawa a hare-haren da suka kai a wurare daban-daban.

Garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ta yi wa yankin Arewacin Najeriya katutu, inda a Arewa maso Yamma abin ya fi tsanani a Jihar Zamfara da Katsina, mahaifar Shugaban Kasar.

Ayyukan ’yan bindiga a Zamfara sun sa Gwamnatin Tarayya haramta shawagin jirgi da ayyukan hakar ma’adinai a Jihar, bisa zargin  amfani da jirage wurin fasakwaurin makamai da kuma hadin baki tsakanin masu hakar ma’adinan da ’yan bindiga.

Kimanin shekara 10 ke nan matsalar ’yan bindiga take addabar Jihar Zamfara, inda abin ya faro daga satar shanu.