✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun sace matafiya 14, sun kashe mutum 4 a Taraba

'Yan bindigar sun tare hanya sannan suka sace matafiya da dama.

Wasu ‘yan bindiga sun sace matafiya 14 a kan hanyar Mutumbiyu Wukari da ke Karamar Hukumar Gassol a Jihar Taraba.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Benbel na Karamar Hukumar da misalin karfe 2 na ranar Lahadin da ta gabata.

‘Yan bindigar da suka kai harin a kan babura, sun tare babbar hanyar da ta ratsa kauyen Benbel, inda suka sace fasinjoji da direbobin ababen hawan da suka yi gamo da bacin rana.

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Benbel, ya shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da jakunkunan fasinjoji da wasu kayayyaki da ke cikin motocin.

Ya ce ‘yan bindigar sun tuntubi ‘yan uwan daya daga cikin direbobin motar suna neman a biya su kudin fansa na Naira miliyan 30.

Ya ce maharan sun kuma tuntubi sauran ‘yan uwan mutanen da suka sace, inda suka bukaci a ba su wasu makudan kudade a matsayin fansa.

Kazalika, an kashe mutum hudu tare da sace mutum shida yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a kasuwar Jauro Manu da ke Karamar Hukumar Gassol da rana tsaka a ranar Lahadi.

An gano cewa ‘yan bindigar kimanin su talatin a kan babura sun kai farmaki kasuwar da misalin karfe 2 na rana, inda suka bude wuta a wurare daban-daban, lamarin da ya yi ajalin mutanen hudu nan take.

Wani mazaunin garin, Umar Tasiu, ya shaida wa Aminiya cewa harin da aka kai ranar Lahadi shi ne na uku a cikin ‘yan kwanakin nan wanda akalla rayukan mutum 12 sun salwanta.

Wakilinmu da ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba, DSP Kwache Bajabu Gambo, ta tabbatar masa da faruwar lamarin.