Yan bindiga sun sace matar soja da wasu mutum 6 a Kaduna | Aminiya

Yan bindiga sun sace matar soja da wasu mutum 6 a Kaduna

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Maryam Ahmadu-Suka Kaduna da Rahima Shehu Dokaji

Mutum bakwai, ciki har da matar wani soja ne aka sace a unguwannin Keke A da B ne aka sace a sabon garin Kaduna (Millenium City) da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakiliyarmu cewa da misalin 11:00 na daren Talata ne ‘yan bindiga suka kai hari unguwar, inda suka shafe kimanin awa guda suna kai farmakin.

Wani dan unguwar Keke A da ya nemi a sakaya sunansa ya ce mutane uku aka sace a unguwar tasu.

“‘Yan bindigar wani babban gida suka nufa a unguwar, kuma gidan na wani soja ne, sai dai ba ya gida a lokacin, amma sun yi awon gaba da matarsa.

“Sun sace makwabcin sojan ma, da ‘yarsa mai shekara takwas, amma kwakwazon mahaifiyarta ya sa sun ajiye ‘yar.

“A wannan lokacin ne ma suka fara harbi kan mai uwa da wabi don kar wani ya yi yunkurin kai dauki, ana cikin haka wani mutum a mota da ke dawowa gida ya fada hannunsu. Shi ne na ukun da suka dauka”, inji mazaunin unguwar.

Ya kuma ce ‘yan unguwar da suka ga haka sun gudu daga unguwar, gudun kar abin ya ritsa da su.

A hannu guda kuwa a unguwar Keke B, ‘yan bindigar sun sace wani mutum, da matarsa, da masu aikinsu biyu.

Da wakiliyarmu ta nemi jin ta bakin kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige kan lamarin, ya ce zai tuntube ta daga bisani.

Sai dai har zuwa lokacin hada rahoton bai yi hakan ba.