✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutane da tsakar rana a Abuja

’Yan bindiga sun sace mutum biyar da babura shida da tsakar rana a hanyar Tekpeshe zuwa Gurdi da ke yankin Birnin Tarayya Abuja.

’Yan bindiga sun sace mutum biyar da babura shida da tsakar rana a hanyar Tekpeshe zuwa Gurdi da ke yankin Birnin Tarayya Abuja.

Kansilan gundumar Gurdi, Wozhe Ishaya, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne bayan ’yan bindigar sun tare hanyar Tekpeshe zuwa Gurdi tare suka sace mutanen da misalin karfe 5:00 na yamma ranar Alhamis.

Ya ce, “Wadanda aka sace din sun je unguwar Tekpeshe ne domin jajanta wa wasu da ’yan bindiga suka sace, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Gurdi a lokacin da suka ci karo da ’yan bindigar,” inji shi.

Ya ce ’yan bindigar wadanda ke rike da manyan makamai sun kuma yi awon gaba da babura shida.

Ishaya, ya bayyana cewa a halin yanzu wasu mazauna kauyen Dadin Kowa da ke kusa da Gurdi na tserewa daga gidajensu saboda fargaba.

“Yanzu da nake magana da ku, wasu mazauna kauyen Dadin Kowa sun fara barin kauyensu bayan da suka ji labarin sabon lamarin.” Inji shi.

Shi ma tsohon Kansilan Gurdi, Mohammed Ibrahim, wanda dan asalin garin Tekpeshe ne, ya ce  mutane biyar tare da babura shida barayin suka sace.

“’Yan fashin sun je karbar kudin fansar wasu da suka yi garkuwa da su a kauyen Zago a makon juya a wurin ne, tsakanin kauyenmu da Gurdi.

“Ana cikin haka sai ga wasu mutanen kauyen da suka baro Tekpeshe a kan babura suna komawa Gurdi, kwatsam suka ci karo da su,” inji shi.

Ba mu samu ji ta bakin Hakimin Gurdi, Alhaji Bala Mohammed, game da faruwar lamarin, saboda bai dauki kiran da muka yi masa ta waya ba.

Kakakin ’yan sandan Babban Birnin Tarayya, DSP Adeh Josephine, har yanzu ba ta amsa sakon da aka aike mata ba game da sabon harin ba.