✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 120 a Zamfara

Sun cimma wannan adadin ne bayan alkaluman da suka dauka daga gida zuwa gida.

Mazauna garin Goran Namaye da ke Jihar Zamfara sun ce yanzu adadin wadanda ’yan bindiga suka sace daga garin ya kai mutum 120.

Mazaunan sun ce sun cimma wannan adadin ne bayan alkaluman da suka dauka daga gida zuwa gida kamar yadda sarkin garin ya bayar da umarnin a yi.

Ibrahim Sulaiman Gora, wani da ya ce an sace mutum tara daga cikin danginsa, ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa maharan sun kwashe sa’o’i suna aikin tattara wadanda za su yi garkuwa da su.

A baya dai ’yan sanda sun ce mutum hudu ne aka kashe kuma aka sace wasu 50 a harin da masu garkuwa da mutane suka kai garin da tsakar daren ranar Lahadi.

Wannan na zuwa ne yayin da a ranar Litinin da ta gabata, mazauna garin Kurar Mota inda a watannin bayan aka kashe ’yan sanda 13, suka ce maharan sun sake shiga garin cikin daren ranar Litinin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutum 50 a garin Goran Namaye da ke Karamar Hukumar Maradun ta jihar.

Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka yayin tattauna wa da manema labarai ranar Litinin a Gusau, babban birnin Jihar.

Shehu, ya ce ’yan bindigar sun farmaki garin cikin daren ranar Lahadi, inda suka kashe mutum hudu sannan suka sace wasu mutum 50.

Sai dai ya ce an baza jami’an tsaro yankin don daukar matakan tsaro da suka dace.

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Zamfara, CP Yakubu Elkana, ya ba da umarnin ceto wanda aka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ya umarci jama’ar yankin da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce jami’an tsaro na aiki don tabbatar an kubutar da wanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.