✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace mutum 16 a kauyen Katsina

Wasu ’yan bindiga a daren jiya na Litinin sun yi awon gaba da akalla mutum 16 yayin da suka kai farmaki kauyen Unguwar Malamai da…

Wasu ’yan bindiga a daren jiya na Litinin sun yi awon gaba da akalla mutum 16 yayin da suka kai farmaki kauyen Unguwar Malamai da ke Karamar Hukumar Danmusa ta jihar Katsina.

Wani mazaunin kauyen ya shaida wa Aminiya ce ’yan bindigar sun yi wa kauyen dirar mikiya ne da tsakar dare a ranar Litinin, inda suka kwashe tsawon awanni suna cin karensu babu babbaka gabanin su debi na diba.

“Sun mamaye kauyenmu na Unguwar Malamai da misalin karfe 11.45 na dare kuma suka kwashe tsawon lokaci suna harbe-harbe.”

“Sun yi awon gaba da mutum 16 ciki har da Mai Garin kauyen, Kabiru Mai Unguwa da matan aure shida, da ‘yan mata uku da kananan yara shida.”

“A wannan lokaci, uku daga cikin ’yan bindigar sun tilasta wani mutum a kan lallai sai ya kais u gidan yayansa a kan babur kuma dole kanwar naki ya aikata abin da suka umarta.”

“Biyu daga cikinsu sun shiga gidan, dayan kuma ya yi dako a bakin kofa, kuma ya umarci wancan mutumin ya kama gabansa bayan ya kawo su gidan.”

“Daga nan ne mutumi ya ruga wurin jami’an tsaro ya fada musu halin da ake ciki a kauyen, amma maimakon su je su tunkari ’yan bindigar, sai suka nemi mutumin da ya tsahirta a wurinsu har zuwa wayewar gari.”

Mai magana da yawun Rundunar ’yan sandan jihar Katsina, SP Isah Gambo, bai tabbatar da faruwar lamarin ba sai dai ya sha alwashin waiwayar manema labarai kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai cika alkawarinsa ba.