✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 3 a wani coci a Kogi

Maharan sun rika harbi a sama don su tsorata mutane da ma jami’an tsaro.

Akalla mutum uku ne ’yan bindiga suka sace a majami’ar Living Faith da ke gundumar Osara a kan hanyar Lakwaja zuwa Okene a Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi.

Aminiya ta gano cewa maharan sun yi wa cocin kawanya ne lokacin da masu ibada suke ciki a karshen mako.

Rahotanni sun ce sun rika harbi a sararin samaniya don su tsorata mazauna yankin da ma jami’an tsaro lokacin da suke kokarin guduwa da mutanen zuwa cikin daji.

Shugaban Karamar Hukumar ta Adavi, Joseph Omuya Salami ne ya tabbatar da satar mutanen ta bakin kakakinsa, Habib Jamiu.

Ya ce tuni Majalisar Karamar Hukumar ta ziyarci yankin tare da rakiyar Baturen ’Yan Sanda (DPO) na yankin Osara, inda ya ce suna kokarin ganin an ceto mutanen.

“Maganar da nake da kai yanzu haka, mun gudanar da taruka da mutanen yankin a kan lamarin inda na ba su shawarar su dakatar da duk wasu taruka da dare na dan wani lokaci.

“Mun ce musu duk kuma wanda zai yi haka ya kamata ya sami amincewar jami’an tsaro, amma suka ki ji,” inji Shugaban Karamar Hukumar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Kogi, CSP Williams Ovye Aya bai amsa kiran da wakilinmu ya yi masa ba ko dawo da amsar rubutaccen sakon da aka aika masa a kan lamarin, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.