✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 50 a Sakkwato

’Yan bindigar sun bude wuta akan daya daga cikin ayarin motocin matafiyan.

‘Yan bindiga sun sace akalla mutane 50 da suka halarci wani taron daurin aure a Jihar Sakkwato yayin da suke komawa Jihar Zamfara a karshen makon nan.

Shaidu sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a Yammacin ranar Asabar, a lokacin da mutanen ’yan Jihar Zamfara ke kokarin komawa gida Gusau bayan halartar wani daurin aure a garin Tambuwal.

A zantawarsa da manema labarai, Shugaban Karamar Hukumar Tureta, Abubakar Salihu, ya ce ’yan bindigar sun yi nasarar kwasar mutanen a tsakanin Karamar Hukumar ta Tureta da ke Jihar Sakkwato da Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara.

Bayanai sun ce ’yan bindigar sun bude wuta akan daya daga cikin ayarin motocin matafiyan, abinda ya tilasta musu tsayawa, inda suka kwashe matafiyan suka gudu da su cikin daji.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara SP Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce a halin yanzu jami’ansu da sauran jami’an hadin gwiwa na gudanar da bincike domin gano sauran wadanda ke hannun ’yan bindigar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, akasarin matafiyan da aka sace masu sana’ar sayar da wayoyin sadarwa ne a kasuwar Bebeji Plaza da ke Jihar Zamfara.

Aminiya ta ruwaito cewa, 20 daga cikin mutanen da aka sace sun kubuta amma sauran 30 din an yi awon gaba da su zuwa daji.

Shugaban masu sanaar sayar da waya reshen Jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Garba Mukhtar ya ce ’yan bindigar sun yi amfani da wayar salula ta daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su wajen kira inda suka sanar cewa mambobinsu 30 na tare da su.

Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya dai na ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga wadanda ke kashe matafiya da mazauna karkara tare da garkuwa da wasu domin karbar kudin fansa.