✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Bindiga Sun Sace Shanu Da Kayan Abinci A Neja

Mutanen sun tsere zuwa garin Wushishi don gujewa ’yan bindigar musamman a harin a ranakun Litinin da Laraba.

Dalilin yawan sace-sacen dabbobi da kayan abinci da ’yan bindiga ke yi a jihohi da dama irinsu Neja, ya sa shanu suka yi karanci a manyan kasuwanni.

Aminiya ta tattauna da Manoma a kauyukan Akare da Tashare Jirgi da kewaye da ke Karamr Hukumar Wushishi ta jihar Neja, in da suka koka kan yadda ’yan bindiga ke sace musu shanu da kayan abinci.

Wani dillalin shanu a Neja Abdulrashid Suleniman, ya bayyanawa Aminiya ta wayar tarho cewa ya bar dillanci saboda hare-hare ga makiyaya, da satar shanun da ’yan bindigar ke yi.

“Yanzu na  koma kananan sana’o’i saboda ko ni satar ta sha rutsawa da ni.

“A da, ina dillancin shanu ba ma a iya Arewa ba har da jihohi irinsu Legas da ke Kudu.

“Nakan sayar da kamar tirela 20 a kasa baki daya a rana, amma yanzu babu shanun ma balle ka sayar.

Shi ma wani mazaunin yankin mai suna Bala Muammad, ya ce da dama daga mutanen sun tsere zuwa garin Wushishi, don gujewa ’yan bindigar, musamman a harin da suka kai musu a ranakun Litinin da Laraba.

A hannu guda mun yi yunkurin ji ta bakin Kwamishina Tsaro da Ayyukan Jinkai na jihar, Emmnuel Umar, amma hakan ya ci tura, kasancewar bai daga waya ba har zuwa lokacin hada rahoton.