✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace shugaban APC a Neja

An sace shi ne yana tsaka da duba aiki a gona.

Wasu ’yan bindiga sun sace shugaban jam’iyyar APC na shiyya ta uku a Karamar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja, Aminu Bobi.

Rahotanni sun ce an sace shi ne da yammacin ranar Asabar lokacin da yake duba masu yi masa aiki a gonarsa.

Wata majiya da ke da kusanci da shugaban ta ce ’yan bindigar sun zo ne a kan babura kimanin shida, kowanne dauke da mutum uku kuma sun rika harbi kan mai uwa da wabi.

Ya ce shugaban APC shi kadai ’yan bindigar suka tafi da shi yayin da basu tafi da kowa daga cikin masu yi masa aikin ba.

Yunkurinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar,  DSP Wasiu Abiodun don tabbatar da harin ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.