✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace Shugaban Karamar Hukuma a Oyo

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukuma tare da direbansa a Jihar Oyo

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Karamar Hukumar Iganna da ke Jihar Oyo, Olayiwola Adeleke tare da direbansa a ranar Lahadi.

Shugaban Karamar Hukumar na tafiya ne a kan hanyar Okeho-Ado Awaye ta zuwa Ibadan don ganawa da Gwamna Seyi Makinde lokacin ’yan bindigar suka sace shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya ya ce, “Bayanan da na samu sun nuna an sace shi ne a kan hanyar Ado Awaye-Iseyin.

“Ana ci gaba da kokarin ganin an sake shi tare da cafke masu laifin”, inji shi.

Da aka tuntube shi, Shugaban kungiyar OPC a jihar, Mista Rotimi Olumo, ya ’yan bindida sun yi garkuwa da Mista Adele ne a yankin Iseyi-Okeho.

Ya ce, “Na kira mutanena kuma sun ce sun fara bincika dazukan da ke yankin don neman shi”