✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun sace tsohowa mai shekara 90 a Zamfara

'Yan bindigar sun yi awon gaba da tsohuwa mai shekara 90 a Karamar Hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wata tsohuwa mai shekara 90 a garin Kurya Madaro dake Karamar Hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Wata majiya a kauyen ta ce, bayan tsohuwar da aka dauke, sun kuma tafi da wasu matasa hudu wanda biyu daga cikinsu yan gida daya ne.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun afkawa garin ne da misalin karfe 12 na daren asabar inda suka yi awon gaba da tsohuwar mai suna Hajiya Aisha bayan da suka gaza kama danta, Alhaji Danbaba, wanda dan kasuwa ne.

“Dan ta suka zo nema, da basu same shi ba dai suka dauki mahaifiyarsa da ba ta iya ko tafiya saboda tsufa,” inji majiyar.

Kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar, SP Muhammad Shehu ya ci tura, saboda rashin samunsa a waya har zuwa lokacin hada wannan rahoto.