✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace dan kasuwa a Jigawa

'Yan sanda sun ce suna kokarin ceto dan kasuwar.

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan kasuwa mai shekara 50, Alhaji Lawan Garba a kauyen Kwadabe da ke Karamar Hukumar Kiyawa ta Jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa, DSP Shiisu Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse, babban birnin jihar.

A cewarsa, “’Yan sanda sun samu labarin ne daga Samariyawa nagari a kauyen da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin.”

Ya kuma bayyana cewa, bayan samun rahoton ne ’yan sanda suka yi gaggawar kai dauki domin ceto wanda lamarin ya rutsa da shi.

Binciken farko ya nuna cewa ’yan bindigar sun tafi da wayoyin hannu guda biyu na mutumin da suka sace.

Shiisu ya bayyana cewa, ’yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen kama duk masu laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Ya bukaci al’ummar Jihar Jigawa da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wasu muhimman bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.