‘Yan bindiga sun sace mara lafiya da ke kan gadon jinya a Zariya | Aminiya

‘Yan bindiga sun sace mara lafiya da ke kan gadon jinya a Zariya

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Abubakar Sadiq Mohd, Zariya da Abubakar Muhammad Usman

‘Yan bindiga sun kai farmaki kauyen Anguwar Malamai da ke Kakeyi a Zariya, inda suka yi awon gaba da wata mata da take jinya a gida.

Anguwar Malamai dai ita ce mafi kusa da shahararriyar madatsar ruwa ta Zariya kuma tana da nisan kilomita 1 daga gidan talabijin na tarayya (NTA) da ke Zariya.

‘Yan bindigar da suka isa kauyen da misalin karfe 12:00 na daren Alhamis, sun zarce zuwa gidan wani Alhaji Shu’aibu Dallatu, inda suka yi garkuwa da matarsa.

Daya daga cikin mutanen kauyen da aka zanta da shi wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce “’Yan bindigar sun zo ne da nufin yin garkuwa da Alhaji Shu’aibu Dallatu, domin da isar su sun tambayi wasu matasa da ke kwana a shago da ke wajen gidan.

“Alhaji Dallatu wanda ya farka don kula da matarsa ​​marar lafiya, ya tsere bayan da fahimci ‘yan bindiga ne suka kawo masa hari.”

Ya kuma bayyana cewa, a lokacin ba su samu mijin ba, sai suka yanke shawarar yin garkuwa da matar, duk da rashin lafiyar da take fama da ita.

“Sun saka ta cikin wata mota, sannan suka fara harbi a iska kafin daga bisani suka sulale.”

Kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, kan lamarin ya ci tura saboda an gaza samun sa a waya.