’Yan bindiga sun sace ’yar uwar Ministar Buhari | Aminiya

’Yan bindiga sun sace ’yar uwar Ministar Buhari

Buhari tare da Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen
Buhari tare da Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen
    Ado Abubakar Musa, Jos da Ishaq Isma’il Musa

Ana fargabar wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Dapit Karen, wata ’yar uwar Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen a Jihar Filato.

Aminiya ta samu cewa lamarin ya auku ne a unguwar Rantiya da ke yakin Rantiya na Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar.

Wani dan uwan wacce lamarin ya ritsa da ita, ya tabbatar wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 5 na safiya yayin da mazauna yankin ke sharar bacci.

Ya ce da zuwan maharan sai suka zarce kai tsaye zuwa gidan wacce lamarin ya ritsa da ita, inda a halin yanzu har sun tuntunbi ’yan uwanta a kan biyan fansar Naira miliyan biyar.

Yayin da wakilanmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, Ubah Gabriel, ya ce ba su da masaniya sai dai ya yi alkawarin bincikar lamarin sannan ya waiwaye shi.