✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sake garkuwa da daliban sakandare a Zamfara

Daliban makarantar na tsaka da rubuta jarabawa aka kai musu hari.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai maza da mata da yawa a wata makarantar sakandare a Karamar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara.

A safiyar Laraba maharan suka yi wa wata makaranta da ke unguwar  Kaya a karamar hukumar kutse, suka yi awon gaba da daliban da ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Wani mazaunin kauyen ya tabbatar cewa maharan sun kutsa kai cikin makarantar ne suna ta harbe-harbe a yayin da dalibai ke tsaka da rubuta jarabawa.

Maharan sun tattare kofofin ajujuwan suka sa daliban su fito wata, amma Allah Ya taimaki wasu daga cikin daliban suka tsere ta taga, suka bobboye a cikin gonaki da ke kusa da makarantar.

Babu cikakken bayani game da yawan daliban da aka yi garkuwa da su, amma wasu majiyoyi na cewa dalibai mata da maharan suka tafi da su sun fi mazan yawa.

Wasu majiyoyi sun ce dalibai kimanin 400 ne ke makarantar a lokacin da ’yan bindigar suka kai farmakin.