Daily Trust Aminiya - ’Yan bindiga sun sake hallaka mutane a Kaduna
Subscribe

’Yan bindiga sun sake hallaka mutane a Kaduna

Mutum biyu sun bakunnci lahira sakamakon harin da ’yan bindiga suka kai kauyen Garu da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna ranar Laraba.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya tabbatar da harin da ya yi sanadiyyar mutuwarA AliyuDaiyabu da kuma Safiyanu Muhammad.

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai na mika ta’aziyya ga iyalansu da iyalan wani mafarauci da aka tsinci gawarsa a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar

Gabanin haka, Aruwan ya ce sojojin rundunar Operation Thunder Strike na ci gaba da aikin sintiri a yankin Gwagwada a Karamar Hukumar Chikun wanda ya hade da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Ya ce aikin sharar dazuka da sojojin suka yi, ya yi nasarar tarwatsa sansanonin ’yan bindiga a Napayako da kuma Dajin Wuya.

Ya ce sojojin sun yi aikin ne bayan ’yan bindiga sun kai wa mafarauta hari a cikin daji, wanda a sanadiyyar hakan mafarauta biyu suka samu raunukan bindiga.

“A lokacin aikin, sojoji sun shiga wurin tare da mafarauta da suka tsira, inda suka watsa sansanonin ’yan bindiga, aka kuma gano wani mafarauci da ya jikkata, Yohanna Yakubu, dayan kuma Isuwa Tanko, ya rasu daga baya,” inji Kwamishinan.

More Stories