✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kaduna

Kwana daya bayan harbe mutane da dama har lahira a karamar Hukumar Kaura, ’yan binduga sun sake kai hari kauyen Kagoro da ke Jihar Kaduna…

Kwana daya bayan harbe mutane da dama har lahira a karamar Hukumar Kaura, ’yan binduga sun sake kai hari kauyen Kagoro da ke Jihar Kaduna a daren Juma’a.

’Yan bindigar sun kai harin ne da karfe 9:00 zuwa 9:45 na dare, inda suka hau harbi kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun zo ne da manyan makamai inda suka hau harbin mutane ba ji ba gani.

“Sai dai ba a samu wanda ya rasa ransa ba, saboda daukin da sojoji suka kawo akan lokaci,” in ji shi.

Sai dai ya zuwa lokacin tattara wannna rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ko hukumomin tsaro kan faruwar lamarin.

Kazalika yunkurin da wakilinmu yayi na ji ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, Muhammed Jalige ya ci tura.