✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Kaduna

Gwamnatin ta tabbatar da cewa dukkan dalibai 307 din da aka yi yunkurin sacewa yanzu haka suna cikin koshin lafiya

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu ’yan bindiga sun kai hari Makarantar Sakandiren Kimiyya dake garin Ikara (SSS Ikara) a Karamar Hukumar Ikara ta jihar da daren ranar Asabar amma sojoji suka dakile yunkurin nasu.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa dukkan dalibai 307 din da aka yi yunkurin sacewa yanzu haka suna cikin koshin lafiya kuma wata hadin gwiwar jami’an tsaro da masu aikin sa kai ne suka sami nasarar ceto su.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gaida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna ranar Lahadi

Ya ce, “Mun dakile yunkurin nasu. Mun yi sa’a daliban sun yi amfani da shawarwarin tsaron da muke ba su wajen ankarar da jami’an tsaro a kan kari. Kuma jami’an tsaro wadanda suka hada da sojoji da ’yan sanda da ma wasu masu aikin sa kai suka garzaya suka cimmus tare da ceto daliban.”

Muna tafe da karin bayani…