✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake kai hari wata makaranta a Kagara, sun sace mutum bakwai

'Yan bindigar sun riski makarantar fayau babu kowa sai fushi ya kama su.

’Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari a garin Kagara da ke Karamar Hukumar Rafi inda suka far wa wata Kwalejin Kimiyya a Jihar Neja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan da suka kai farmaki makarantar a ranar Lahadi da dare sun riske ta fayau babu kowa.

A makon jiya ne Gwamnatin Neja ta bayar da umarnin rufe kafatanin makarantun kwana da ke Jihar bayan sace dalibai da wasu malamai da ma’aikatan makarantar sakandaren maza zalla ta GSSS Kagara.

’Yan bindigar da a yanzu suka tsiro da sabon salon kai wa makarantun kwana hari su yashe dalibai, sun riski makarantar fayau lamarin da ya fusata su suka afka wani kauye da ke kusa inda suka yi awon gaba da mutum bakwai.

Majiyar ta shaida wa Aminiya cewa, “sun samu makarantar babu kowa a yayin da tuni dalibai da malamansu suka kaurace wa makarantun kwana bayan umarnin da gwamnatin jihar ta bayar.”

Daga cikin wadanda ’yan bindigar suka sace akwai wani Alhaji Aminu, Darakta a kamfanin ruwa na Kongwama.

Wannan lamari na zuwa ne bayan sako dalibai da malaman GSC Kagara da ’yan bindiga suka sace kwanaki goma da suka gabata.

Kazalika, ’yan bindiga sun sake kai hari wasu kauyukan Kagara jim kadan bayan sako daliban inda suka kashe akalla mutum hudu.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wa ’yan bindiga masu tayar a zaune musamman a yankunan Arewa gargadin su sani cewa basu fi karfin gwamnatinsa ba.

Shugaban Kasar ya ce jami’an tsaron kasar na iya murkushe su a lokaci guda sai dai gwamnatinsa na la’akari ne da rayukan mutanen da za su salwanta wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.