✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sake sace mutane a Zariya

Harin farko ke nan a yankin Wciciri da ke Gabashin Karamar Hukumar Zariya.

’Yan bindiga sun sace matafiya da ba a san adadinsu ba a yankin Wuciciri na Karamar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.

Wannan shi ne karo na farko da mahara suka kai farmaki a yankin da ke Gabashin karamar hukumar.

Kafin yanzu ’yan bindiga sun saba kai farmaki tare da yin ayyukansu ne ta bangaren Yammacin karamar hukumar, wato gundumar Dutsen Abba.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun kai farmakin ne da misalin karfe 10 na daren ranar Talata, inda suka sace mutum biyu; Alhaki Nazifi da kuma Alhaji Shafiu Broda.

“Sun bude wa wata motar haya wuta, sannan suka yi awon gaba da fasinjojin cikinta gaba daya, ba mu san adadin mutanen da ke cikin motar ba, amma maharan ba su kashe kowa ba,” a cewarsa.

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ya yi alkawarin bincikar gaskiyar lamarin domin yi wa wakilinmu karin bayani, amma har yanzu bai sake waiwayar mu ba.