✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun saki sabon bidiyon daliban Kwalejin Afaka

Bidiyon ya nuna matar soja da aka yi garkuwa da ita, daliban na rokon a cece su

’yan bindigar da suka sace daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka, Jihar Kaduna, sun saki sabon bidiyon ragowar dalibai 29 da ke hannunsu.

Karo na biyu ke nan ’yan bindigar suna sakin bidiyon da ke nuna halin da daliban suke ciki bayan kwana 47 a hannunsu.

A bidiyon da suka saki ranar Litinin da dare, daliban, cikinsu har a wata mai juna biyu, na cewa, “Muna rokon iyayenmu su taimake mu saboda muna cikin wani hali kuma babu abinci.

“Su taimaka su yi iya kokarinsu su fitar da mu daga wannan wuri; kwananmu 47 ke nan, ga shi kusan dukkanninmu ba mu da lafiya kuma a fili muke kwana, ko da ruwan sama ake yi,” inji mai juna biyun.

A sabon bidiyon, ’yan bindigar da ke magana da harshen Hausa da Fulatanci, sun nuna wata mata da suka ce mijinta soja ne kuma sun yi awon gaba da ita ne a Tirkania-Agwa da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Matar da ta ce mijinta jami’in Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ne da ke aiki a Warri, ta roki Gwamnatin Tarayya ta kubutar da su, inda ta ce masu garkuwar na neman kudin fansa Naira miliyan 30 kafin su sake su.

Sakin bididon na zuwa ne kimanin mako uku bayan sakin 10 daga cikin daliban da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su a kwalejin, wadanda suke neman kudin fansa Naira miliyan 500, kafin daga bisani su rage zuwa Naira miliyan 300.