✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sako basarake da suka sace a Neja

Mace ce jagorar ’yan bindigar da suka yi garkuwa da Etsu Jibi a Neja.

’Yan bindiga da wata mace take jagoranta sun sako wani basaraken da suka yi garkuwa da shi a Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Neja, Malam Muhammadu Dahiru.

An yi garkuwa da Malam Muhammadu Dahiru, wanda shi ne Esu Jibi a Karamar Hukumar ne kimanin mako biyu da suka gabata.

ِAminiya ta gano cewa gungun wasu ’yan bindiga da wata mace take jagoranta ne suka kutsa fadar Etsu Jibi da misalin karfe 11 na dare, inda suka jikkata ’yan banga biyu sannan suka yi awon gaban da basaraken.

– Mun kwana muna tafiya

Kanin Etsu Jibi, Ibrahim Dahiru, ya shaida mana cewa ’yan bindigar sun kira shi ranar Laraba suna neman a kai musu kudin fansar basaraken Naira miliyan 15.

“Na je garin Jere a kan babur, daga nan na shiga wani kungurmin jeji da ke kusa da Kubacha a Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna inda na hadu da su.

“A nan suka kwace babur din nawa, suka kuma tsare ni, ba su suka sako ni ba, sai da misalin karfe 11 na dare, inda suka umarce mu tashi mu tafi tare da Esu.

“Mun kwana muna tafiya a kafa, da gari ya waye sai muka samu wani mai babur din haya ya kai mu bakin babban titi, kafin mu iso gida ranar Alhamis da maraice,” inji Ibrahim.