✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako Daliban Bethel Baptist 32

Har yanzu sauran daliban makarantar na hannun masu garkuwar.

’Yan bindiga sun kara sako 32 daga cikin daliban da suka yi garkuwa da su a makarantar Betel Baptist High School, da ke Jihar Kaduna.

Kawo yanzu dalibai 90 ke nan suka shaki iskar ’yanci daga cikin dalibai 121 da ’yan binidga suka yi garkuwa da su a makarantar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da sakin daliban na Bethel Baptist su 32.

Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), Reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya ce: “Gaskiya ne, an sako 32 daga cikin dalibanmu a yammacin Juma’a.

“Amma har yanzu akwai ragoar dalibai 31 a hannun wadanda suka yi garkuwa da su kuma muna addu’ar su ma a sake su nan ba da jimawa ba ”, inji shi.

A safiyar ranar 5 ga watan Yuli ne ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar Bethel Baptist da ke Maraban Damishi a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, suka yi garkuwa da daliban makarantar 121.

Daga baya suka saki rukunin farko na dalibai 58 kafin wadanda suka sako a yanzu. Wasu daga cikin daliban sun tsere ne daga hannun ’yan bindigar.

An sako daliban na Bethel Baptist ne ’yan sa’o’i bayan masu garkuwa da mutane sun sako daliban Makarantar Islamiyyar Salihu Tanko da ke garin Tegina da ke hannunsu.

An sako daliban Islamiyyar ta Tegina ne bayan sun shafe kusan wata uku a hannun masu garkuwar kuma bayan biyan kudin fansa kimamin Naira miliyan 68.

A ranar ce kuma ’yan bindiga suka sako daliban da suka yi garkuwa da su a kwalejin binciken kimiyyar noma da ke Jihar Zamfara.