✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako Mataimakin Shugaban Hukumar Shige da Fice

An sako shi tare da wasu mutum hudu bayan biyan kudin fansa.

Mataimakin Shugaban Hukumar Shige da Fice, Alhaji Danladi Idris Boris (Mai Ritaya) da wasu mutum hudu sun shaki iskar ’yanci daga hannun masu garkuwa da mutane bayan biyan kudin fansa.

An yi garkuwa da tsohon jami’in hukumar ne a ranar Lahadi a Unguwar Dabiri da ke yankin Tungan-Maje a Karamar Hukumar Gwagwalada, Abuja.

Daya daga cikin iyalansa ya ce, “Mun dauko su a wani daji da ke Paiko a Jihar Neja, bayan biyan wasu kudi. Amma ba zan bayyana nawa aka biya ba saboda tsaro.”

Majiyar ta ce an sako shi ne tare da dansa da wasu mutum uku da misalin karfe 7 na dare.

Sai dai mai magana da yawun ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ba ta amsa kiran wayar wakilinmu ba, balantana a ji ta bakinta game da lamarin.