✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako 11 daga cikin fasinjojin da suka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna

Mutum 11 daga cikin 62 sun kubuta bayan shafe kwanaki 74 a tsare.

’Yan bindiga sun sako wasu mutum 11 daga cikin fasinjoji 62 da suka yi garkuwa da su a harin da suka kai wa wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris na bana.

Aminiya ta ruwaito cewa bayan shafe kwanaki 74 a hannun wadanda suka yi garkuwa da su, mutum 11 da suka hada da mata shida da maza biyar sun shaki iskar ’yanci a ranar Asabar.

Mawallafin Jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, wanda ya shiga tsakani, ya bayyana wa wakilanmu sunayen mutanen da suka kubuta da suka hada da Amina Ba’aba Mohammed, Rashida Yusuf Busari, Jessey John, Hannah Ajewole, Amina Jibril da kuma Najib Mohammed Dahiru.

Sauran sun hada da Hassan Aliyu, Peace A. Boy, Danjuma Sa’idu da Gaius Gambo; sai dai Mamu bai bayyana sunan mutum cikon na 11 ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Sai dai Mamu ya ce majiyoyinsa sun tabbatar masa da cewa, ‘yan ta’addan sun sako mazan biyar daga cikin wadanda ke hannunsu bisa la’akari da rashin lafiyar da suke fama da ita, yayin da matan da aka sako sun kasance masu rauni wanda hakan na cikin yarjejeniyar da aka kulla da wadanda suka yi garkuwar da su.

Mamu ya ce, “Yayin da muke ci gaba da tattaunawa da ’yan bindigar, mun yi tsammanin za a sako dukkan matan da aka yi garkuwa da su a wannan rukuni na farko da suka kubuta a yanzu.

“Amma daga bisani sun rage adadin matan da za su saki saboda Gwamnatin Najeriya ta bukaci a hada da masu fama da matsananciyar rashin lafiya a cikin rukunin farko na wadanda za su sako.

Hakazalika ya ce babban malamin Islama da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, shi ma ya taka rawa ta bayan fage.

An kai mutanen da aka sako wani asibiti da ke birnin tarayya Abuja don jinyar.

Wakilanmu da suka tuntubi wasu daga cikin ‘yan uwan fasinjojin da aka sace, sun samu cewa ba su da masaniya game da wannan lamari na baya bayan nan amma dai har yanzu ba su debe tsammanin ganin sun dawo gare su ba.

Aminiya ta ruwaito cewa tun bayan harin da aka kai a ranar 28 ga Maris din da ya gabata, ’yan ta’addan sun sako mutane biyu ne kacal daga cikin wadanda suka yi garkuwar da su.

Daya daga cikin wadanda ’yan bindigar suka saki shi ne Alwan Hassan, Manajan Darakta na Bankin Noma da rahotanni suka bayyana cewa ya biya kusan Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa, sai kuma daga bisani, wata mata mai juna biyu da aka ce sun sake ta saboda tausayi.

Tun da farko dai masu garkuwa da mutanen sun bukaci a sako ’ya’yansu takwas da bayanai ke cewa Gwamnatin Tarayya na tsare da su.