’Yan bindiga sun tare hanya tare da yin garkuwa da mutane a Kano | Aminiya

’Yan bindiga sun tare hanya tare da yin garkuwa da mutane a Kano

’Yan bindiga dauke da manyan makamai sun sanya shinge tare da tare hanyar Dajin Falgore da ke Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano, inda suka yi garkuwa da mutum uku.

Wani ganau ya shaida wa Gidan Rediyon Freedom cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar Litinin, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Shaidan ya kara da cewa matafiya da dama sun ji rauni, cikinsu har da Kwamdan Hisbah na Karamar Hukumar Doguwa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka fara bincike.

A watan Yuli ne Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar Kano, CP Habu Sani ya kai ziyara a yankin na dajin Falgore, inda ya gargadi ’yan sanda da su sa ido sosai musamman a hanyar Kano zuwa Kaduna da Kano zuwa Filato da ke yankin dajin.

A da can, Jihar Kano ba a cika fama da matsalar sace mutane ba, duk da cewa a kan samu lokuta da dama da ake kama masu sace mutane a jihar, ko kuma a karbo wanda aka sata.