✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun tashi kauyuka 5, sun sace shanu sama da 100 a Sakkwato

Dukkan ƙauyukan dai na karamar hukumar Kebbe ne da ke jihar

’Yan bindiga sun fatattaki dubban mutane daga kauyuka biyar, sannan sun sace musu shanu sama da 100 a jihar Sakkwato.

Kauyukkan da lamarin ya shafa sun hada da Ungusi da Asarara da Sangi da Mai Kurfana da kuma Gwandi, dukkansu a karamar hukumar Kebbe ta jihar.

Wata majiya a yankin ta ce ’yan bindigar sun kuma kori al’ummomi da yawa daga karamar hukumar daga muhallansu.

Majiyar ta ce tana kyautata zaton ’yan bindigar sun fito ne daga jihohin Zamfara da Kebbi da Neja da ke makwabtaka da Sakkwaton, inda ake ci gaba da gudanar da ayyukan soji.

Bayanai ba nuni da cewa yanzu haka ’yan bindigar sun sami mafaka a Kebbe a saboda ciyayij da ke yankin.

Majiyar ta kara da cewa lamarin ya zama ruwan dare a kowace shekara a karamar hukumar, inda ’yan bindigar suke zuwa suna addabar kauyukan, suna sace musu dabbobi da amfanin gona tare da raba da dama daga muhallansu.

Ya kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta sa baki ta hanyar aikin soja kamar yadda ta yi shekaru uku da suka wuce.

Wata majiyar ta daban kuma ta ce a ko a ranar Talata sai da ’yan bindigar suka koma Gwandi, inda suka hana mutane girbin amfanin gonarsu, bayan sace masu shanun da suka yi.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, ya ce bai da masaniya kan harin na Talata a Gwandi, amma na baya zai tuntubi wakilinmu daga bisani.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai kai ga yin hakan ba.