✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban Kwalejin Ilimi ta Kaduna guda 4

An sace daliban ne a daren Litinin din da ta gabata

Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai guda hudu na Kwalejin Ilimi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya a Karamar Hukumar Jama’a.

An rutsa da daliban ne a kauyen Mile 1 da ke yankin Gidan Waya da misalin karfe 8:00 na daren Litinin, inda aka yi awon gaba da su, kamar yadda majiyar Aminiya ta tabbatar.

A cikin takardar sanarwar da Kakakin Kungiyar Dalibai ta Jihar Kaduna reshen Kwalejin, Benjamin Fie, ya ce ’yan bindigar sun kira waya inda suke neman wasu makudan kudade kafin su sako su.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana ko nawa suka bukata ba.

“Muna masu bakin cikin sanar da kame daliban Kwalejin Ilmi ta Jihar Kaduna da ke Gidan Waya, inda ’yan bindigar suka bukaci wasu makudan kudade a kansu. Don haka muna bukatar addu’arku a kan lamarin,” inji sanarwar

Daliban da aka kama sun hada da; Racheal Edwin na sashen karatun Biology/Geography da Esther Ishaya na sashen Economic/History da Promise Tanimu na sashen English/History sai kuma Beauty Luka na sashen Spe/CRS.