✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 3 a Zariya

Maharan sun farmaki yankin da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi.

Akalla mutum uku wasu ’yan bindiga suka sace a ranar Lahadi, yayin da suka farmaki yankin mazabar Dembo da ke Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta gano cewar maharan sun farmaki yankin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar, inda suka sace mutanen da suka hada da Alhaji Ali Nura da Alhaji Lawal Musa da kuma Alhaji Sahabi Rufa’i.

Wani ganau a yankin, ya shaida wa wakilinmu cewar, wani mai suna Hudu Shuraibu mai shekara 21 a duniya kuma ya samu rauni sakamakon harbinsa da maharan suka yi a kirji.

Idan ba a manta ba ayyukan ’yan bindiga na ci gaba da kamari a cikin yankunan da ke Karamar Hukumar Zariya, a baya bayan nan.

Hakan ya sanya malaman addinin Musulunci da na Kiristanci gabatar da addu’o’in samun zaman lafiya, bayan umarnin Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli.

Sai dai kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin ’Yan Sandan Jihar, ASP Mohammed Jalige , ya ci tura sakamakon wayarsa na kashe zuwa lokacin hada wannan rahoto.