✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘yan bindiga sun sace basarake da fadawansa

’Yan bindigar sun yi awon gaba da basaraken da fadawansa a yayin da suke dawowa daga wurin biki

An yi garkuwa da , Eze Charles Iroegbu, basaraken Umueze da ke yankin Nguru a karamar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo.

’Yan bindigar sun yi garkuwa da basaraken da fadawansa ne a kan titin Mbano zuwa Mbaise, yayin da suke kan hanyar dawo wa daga wani bikin gargajiya da suka halarta a ranar Laraba .

Zuwa wannan lokaci na hada wannan rahoton ba a bayyana adadin fadawan da aka sace yayin garkuwa da basaraken ba.

Wata majiya a Nguru, ta bayyana cewa lamarin ya jefa mazauna yankin sun shiga cikin dimuwa.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, SP Orlando Ikeokwu, sai dai hakar ba ta cimma ruwa ba.