✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da budurwa a Kebbi

’Yan Sanda sun tabbatar da garkuwa da wata budurwa mai shekara 18 da sanyin safiyar Juma’a a unguwar Gangaren NEPA da ke garin Birnin Kebbi,…

’Yan Sanda sun tabbatar da garkuwa da wata budurwa mai shekara 18 da sanyin safiyar Juma’a a unguwar Gangaren NEPA da ke garin Birnin Kebbi, Jihar Kebbi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi, DSP Nafi’u Abubakar ya tabbatar wa manema labarai hakan a Birnin Kebbi.

Abubakar ya ce ’yan sanda na kokarin ganin an kubutar da budurwar daga lamarin da  ya ritsa da ita.

Ya kuma bukaci jama’a da su taimaka da bayanan da za su taimaka wajen samun nasarar ceto baiwar Allar.

Rundunar ta kuma roki jama’ar jihar da su kai wa jami’an tsaro rahoton duk wata alama da ke da alaka da barazanar tsaro don daukar matakin da ya dace.