✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da malamai a Neja

Sun bi gidajen malamai da dakunan kwanan dalibai suka tisa keyarsu a makarantar gwamnati da ke Kagara

’Yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da dalibai da  malaman Kwalejin Kimiyya ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kagara a Jihar Neja.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai malaman ne zuwa cikin daji bayan sun kutsa gidajen malamai da dakunan kwanan dalibai a makarantar da ke hedikwatar Karamar Hukumar Rafi ta jihar da ke makwabtaka da Birnin Tarayya, da misalin karfe biyu na dare.

Wani shaida ya da maharan sun bindige wani dalibi da ya yi yunkurin tserewa a lokacin da suka kai harin da talatainin dare.

Daya daga cikin tsoffin daliban makarantar, Sanata Shehu, ya ruwaito cewa Shugaban Makarantar ya tabbatar masa da faruwar harin a safiyar Laraba.

Adadin wadanda aka sace

Hukumomin makarantar na ci gaba da daukar bayanan wadanda suka rage a makarantar domin tantance adadin wadanda da aka yi garkuwa da su.

Wata majiya ta ce daya daga cikin ma’iakatan makarantar ya samu ya tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Ta ce wandada aka yi karguwa da su sun hada da Lawal, Ali, Hannatu  tare da mijinta, Dodo, da kuma Mohammed Abubakar(Akawu).

Tuni dai jami’an tsaro suka bazama bin sawun ’yan bindigar yayin da jirgin soji ke ta shawagi a sararin samaniya domin gano inda maharan suka yi da daliban da malaman.

Garkuwa da mutane ya yi kamari a Neja

Hakan ta faru ne kwana biyu bayan an yi garkuwa da fasinjoji 21 da tsakar rana a ganin Minna, Hedikwatar Jihar ta Neja, inda ayyukan masu ’yan bindiga ke ta karuwa a baya-bayan nan.

Bayan labarin sakin fasinjojin a ranar Talata, an kuma samu labarin karin garkuwa da mutane a Jihar mai makwabtaka da Jihar Kaduna da sauran dazuka da ke zama matattarar ’yan bindiga.

Ayyukan masu garku wa da mutane sun addabi mutane a sassan Najeriya tare da sanadin asarar dimbin rayuka da dukiyoyi.

A baya bayan-bayan nan ’yan bindiga da dalibai 344 a Makarantar Sakandaren Kimiyya da ke garin Kankara a Jihar Shugaba Buhari ta Katsina kafin su sako daliban bayan kwana biyar.

’Yan bindiga sun kuma taba kai hare-hare a makantun sakandaren Gwamnati da ke Dapchi Jihar Jobe, Chibok a Jihar Borno suka kuma yi awon gaba da daruruwan dalibai.