✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami’a a Binuwai

Hukumar gudanarwar jami'ar tarayyar na kokarin tantance adadin daliban da aka dauke

’Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai a Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya (FAUM) da ke Makurdi a Jihar Binuwai.

Hukumar gudanarwar Jami’ar ta tabbatar a safiyar Litinin cewa ’yan bindigar sun yi awon gaba da daliban ne da bakin bindiga ranar Lahadi.

Sanarwar da kakakin Jami’ar, Rosemary Waku, ta fitar a safiyar Litinin ta ce, “An yi awon gaba da daliban da ba a san adadinsu ba daga FUAM da bakin bindiga a ranar Lahadi, 25 ga Afrilu, 2021.”

Ta kar da cewa tun daga lokacin hukumar gudanarwar, “Jami’ar ba ta ji duriyar daliban ko wadanda suka yi garkuwa da su ba.”

Sai dai ta ce kawo yanzu dai an sanar da hukumomin tsaro game da abin da ya faru.

Sace daliban jam’iar na zuwa ne kimanin mako guda da sace wasu dalibai da ma’aikata a Jami’ar Greenfield da ke Jihar Kaduna, wadanda daga baya masu garkuwar suka jefar da gawarwarkin uku daga cikinsu a kusa da jami’ar.

Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta Greenfield ta bayyana cewa masu garkuwa da daliban sun tuntube ta suna neman kudin fansa Naira miliyan 800, wanda ya fi karfinta.

Sai dai tun da farko Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da tattaunawa ko biyan kudin fansa ga ’yan bindiga, sannan ta yi barazanar hukunta masu yin hakan da sunanta.

Ta bayyana hakan ne bayan masu garkuwar da mutane sun sace dalibai 39 a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka a Jihar, inda suka bukaci kudin fansa Naira miliyan 500.

Kawo yanzu dai, masu garkuwar sun sako 10 daga cikin daliban kwalejin, bayan iyayensu sun biya kudin fansa.

Iyayen daliban sun ce sun biya kudin fansar ne domin a sako daliban gaba daya, amma masu garkuwar suka sako 10 daga cikinsu.