✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan Kansila a Abuja

'Yan bindigar sun bukaci a basu miliyan 200 kudin fansa.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matan kansilan Mazabar Gwako da ke Karamar Hukumar Gwagwalada, Abuja.

’Yan bindigar da suka kai hari gidan kansilan sun yi garkuwa da matansa biyu, da kanwarsa da kuma kaninsa.

“Daga baya an gano masu garkuwa ne, sun yi awon gaba da matansa biyu, kanwarsa da kuma kaninsa.

“Bayan tattaunawa da su, masu garkuwar sun rage kudin fansar da suke nema daga miliyan 100 zuwa miliyan 15,” cewar wani mazaunin yankin.

Ya ce masu garkuwar sun shiga kauyen ne da misalin karfe 12:08 na dare suna harbi a iska, suka balle kofar gidan kansilan, kafin su yi awon gaba da iyalan kansilan wanda ya samu ya tsere.

A cewarsa, iyalan sun yi magana da masu garkuwar, kuma daya daga cikin matan kansilan tana dauke da tsohon ciki.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto kakakin ’yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf ba ta amsa kiran da wakilinmu ya yi mata ba.