✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da kansila a Edo

Bayan yin garkuwa da Kansilan an gano cewa an yi garkuwa da wani malamin makaranta a wajen.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da Kansilan dake wakiltar mazabar Ewohimi a Karamar Hukumar Esan ta Kudu maso Gabas ta jihar Edo, Hon Israel Inyanabor. 

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da Kansilan ne a ranar Talata akan hanyar Ewatto-Ubiaja-Okhuesan kusa da kogin Ena na karamar hukumar.

An kuma gano cewa an sace Israel a daidai wurin da aka yi garkuwa da wani malamin makaranta, Mista Aluola da matarsa ​​a ranar Litinin.

Mista Israel dai na tsaka tuki ne a kan hanyar Ewohimi lokacin da wasu ’yan bindiga ba zato ba tsammani suka fito daga daji suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya tilasta mishi tsayawa.

Daga nan ne masu garkuwar suka sace shi zuwa cikin daji inda suka saba garkuwa da mutane.

Aminiya ta gano cewa a cikin sa’a 48 an sace mutane uku, Mista Aluola da matarsa ​​da Inyanabor a kan hanyar.

A yanzu haka dai mazauna yankin na rokon a tura rundunar tsaron hadin gwiwa zuwa yankin saboda bata-garin da suka addabe su.

Sai dai duk yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Chidi Nwanbuzor game da faruwar lamarin ya ci tura.