Daily Trust Aminiya - ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan fasa dutse
Subscribe

‘Yan Bindiga

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan fasa dutse

Wasu ma’aikata fasa dutse sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a yankin Idi Ayunre, a garin Ibadan da ke jihar Oyo.

Yankin da ake aikin fasa dutsen na kan titin Ibadan zuwa Ijebu-Ode, a Karamar Hukumar Oluyole a jihar.

Kakakin ’yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da faruwa lamarin, kuma tuni jami’an tsaro suka bi sahun ’yan bindigar.

Ya kara da cewa Rundunar ’Yan SandanJihar ta yi hadin gwiwa da mafarauta don kamo masu garkuwa da ma’aikatan fasa dutsen.

Wani daga ciki ma’aikatan da ya tsallake rijiya da baya, ya Tope Solomon ya bayyana cewa ’yan bindiga sun kai farmaki wajen da suke aikin da ne misalin karfe 3 na yammacin ranar Laraba.

More Stories