✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun yi garkuwa da mai gari da karin mutum 9 a Katsina

’Yan sanda a jihar Katsina sun tabbatar da harin ’yan bindiga a kauyen Gamji na Sabuwa dake jihar inda suka sace akalla mutum 10.

’Yan sanda a jihar Katsina sun tabbatar da harin ’yan bindiga a kauyen Gamji na Karamar Hukumar Sabuwa dake jihar inda suka sace akalla mutum 10.

Cikin wadanda aka sace din har da Dagacin kauyen na Gamji, Malam Falalu Galadima da kuma wani dalibi dake karatun Aikin Shari’a a Makarantar Horar da Lauyoyi dake birnin Yenagoa a jihar Bayelsa, Mahdi Abdussalam.

Kakakin Rundunar  a Jihar Katsina, SP Gambo Isa shine ya tabbatar wa da Aminiya faruwar lamarin a aranar Laraba.

“Muna da jerin sunayen duk mutanen da aka sace, kuma tuni Kwamishinan ’Yan Sanda ya umarci Babban Baturen ‘Yan Sanda na yankin da ya dukufa wajen gano su, kuma yanzu haka dakarunmu sun fantsama cikin daji domin ganin sun ceto su cikin aminci,” inji Gambo.

To sai dai wani mazaunin yankin wanda ya yi magana da Aminiya amma ba ya son a bayyana sunansa ya ce ’yan bindigar sun shiga garin ne da misalin karfe 1:30 na safiyar ranar Laraba tare da bude wuta a kan mutanen da suka sace.

A cewarsa, “Ya zuwa yanzu mun kirga mutum 13 da aka sace, dukkansu maza, ciki har da Dagaci da kuma wani mai karatun aikin lauya wanda a da dalibi na ne a makarantar sakandire.

“Da farko dai mutum 26 suka sace, amma kafin su shiga dajin suka tsaya suka tantance tare da wucewa da 13 daga ciki, sauran kuma suka koro su gida,” inji majiyar.