’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 8 a Neja | Aminiya

’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 8 a Neja

‘Yan bindiga
‘Yan bindiga
    Ishaq Isma’il Musa da Abubakar Akote, Minna

’Yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutane takwas a yayin da suke gudanar da ibada a kauyen Gidigori da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Aminiya ta ruwaito wata majiya a garin tana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu.

Majiyar ta bayyana cewar limamin cocin Salama Baptist Church na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Bayanai sun ce cocin na kusa da yankin Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

A Juma’ar da ta gabata ce wani abu da ake kyautata zaton bam ne ya sake fashewa a kauyen Galadiman-Kogo da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Fashewar na zuwa ne kwana biyar da tashin wani bam din a yankin, wanda ya yi sanadin rasuwar jami’an Hukumar tsaro ta NSCDC su hudu.