’Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Anambra | Aminiya

’Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon dan majalisar Anambra

    Titus Eleweke Awka da Abubakar Muhammad Usman

Wasu ’yan bindiga a karamar hukumar Ihiala da ke Jihar Anambra sun yi garkuwa da tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar, Honarabul Benson Nwawulu.

Wata majiya a yankin, ta ce Nwawulu, dan majalisar da ya yi wa’adi biyu a majalisar dokokin jihar an yi garkuwa da shi a gidansa da ke Ihiala a ranar Lahadi.

Nwawulu dai ya bar majalisar Anambra ne a 2019 domin ya tsaya takarar Majalisar Wakilai, amma bai yi nasara ba.

Sai dai ba a bayyana cikakken bayani game da sace shi ba tun ranar Lahadin da ta gabata.

Aminiya ta gano cewa tsohon dan majalisar ya tuntubi wasu ’yan majalisar jihar na yanzu wadanda abokan aikinsa ne domin neman kudi.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Toochukwu Ikenga, ya tabbatar da sace shi.

Ya kuma ce suna kokarin ganin cewa ya kubuta.

“Eh, an yi garkuwa da shi a ranar Lahadi, kuma muna aiki don ganin mun ceto shi.

“Za a kubutar da shi nan ba da jimawa ba,” inji shi.