✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wanda ya kai kudin fansar basarake a Kano

’Yan bindigar sun rike wanda ya kai kudin fansar basaraken Kano da suka sace.

Hakimin Karfi da ke Karamar Hukumar Takai ta Jihar Kano, Abdulyahyah Ilo, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da shi, inda kuma suka rike wanda ya kai musu kudin fansar basaraken.

Wadanda suka yi garkuwa da shi sun rike Mataimakin Farfesa na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KSTU) da ke Wudil, Huzaifa Karfi, wanda ya je kai kudin fansa.

Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun kashe mutum shida da suka yi kokarin ceto basaraken a lokacin da suka yi awon gaba da shi.

An ce sun mamaye kauyen ne a kan babura daga Jihar Bauchi ta dajin Ringim da ke Jihar Jigawa.

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sa’ad, ya tabbatar da sakin basaraken da masu garkuwa da shi suka yi.

Ya bayyana cewa mafarauta da ’yan banga sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a cikin daji dangane da sace-sacen da aka yi a kauyen na Karfi.

“Sun yi nasarar karbar kudin fansa tare da tsare Dokta Huzaifa; sun bukaci a sako mutuminsu da aka aka kama a matsayin sharadin sakin shi.”

Wani dan uwa ga basaraken, Yusuf Ismail, ya tabbatar da cewa sun sake shi kuma yana asibiti inda yake ci gaba da murmurewa.

Da aka tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, bai iya tabbatar da faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin yin karin haske nan gaba.