✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa dan tsohon Ministan lafiya a Oyo

Hukumar ’yan sandan jihar Oyo a yau Laraba ta tabbatar da yin garkuwa da dan tsohon Ministan lafiya da wa’adinsa ya kare watan da ya…

Hukumar ’yan sandan jihar Oyo a yau Laraba ta tabbatar da yin garkuwa da dan tsohon Ministan lafiya da wa’adinsa ya kare watan da ya wuce Farfesa Isaac Adewole, kusa da unguwar Fiditi a karamar hukumar Afijio da ke jihar Oyo.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Mista Olugbenga Fadeyi, ne ya sanar da hakan ga manema labarai yau a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Mista Olugbenga, ya ce sun samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga su hudu ne suka yi garkuwa Dayo Adewole da misalin karfe 6:30 na yamma a unguwar Iroko.