✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi wa garin Jibiya kawanya

Rahotanni sun ce sai bayan da maharan suka tsere jami'an tsaro suka shiga garin Gurbin Magarya

Gungun wasu ’yan bindiga sun yi wa garin Jibiya da ke Jihar Katsina kawanya a cikin dare, suna neman mamaye garin ta kusurwa biyu.

A ranar Asabar da misalin karfe 9 na dare ne suka kaddamar da harin, amma jama’ar gari suka fito suka dakile yunkurin, wanda shi ne irinsa na uku da barayin na yi.

Korar ’yan bindigar da jama’a gari suka yi ya sa suka far wa kauyen Gurbin Magarya, a kusa da garin na Jibiya, suka kashe mutum uku suka jikkata wasu uku, wadanda yanzu suke karbar magani a asibitin Jibiya.

Majiyar Aminiya ta shaida mata cewa a lokacin da ’yan bindigar ke wannan aika-aika, an sanar da jami’an tsaro game da taruwarsu a hanyar garin ’Yangayya da kuma wajen Dam din Jibiyar.

Majiyar ta ce amma har bata-garin suka shigo mutanen garin suka fatattake su, ba a ga keyar jami’in tsaron ba.

Majiyar tace, jami’an tsaro sun nufi hanyar garin Gurbin amma ba su isa inda maharan suke ba suka toge a wajen garin.

Su kuma barayin suka ci karensu babu babbaka a garin, suka kwashi dabbobi da kayan abinci da dukiya suka tafi abin su, sai bayan sun tafi jami’an tsaron suka shiga garin.

Cikakken rahoto na tafe bayan kammala binciken da muke gudanarwa, domin har zuwa turo wannan labarin ba mu samu jin ta bakin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandar Jihar Katsina ba, domin cin tura da yunkurin namu ya samu.