✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi wa makiyayan Kebbi fashin shanu 2,000 a Sakkwato

Makiyayan na hanyar komawa gida daga yankin Borgu ne ’yan bindiga suka kai musu hari suka kora dabbobin zuwa dajin Zamfara

’Yan bindiga sun tare wasu makiyaya ’yan asalin Jihar Kebbi tare yi musu fashin shanu akalla 2,000 a Jihar Sakkwato.

Makiyayan na hanyarsu ta komawa gida ne ’yan bindigar suke tare su suke kwace musu dabbobi suka kai maboyarsu da ke cikin daji a Jihar Zamfara.

Sakataren Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah na Jihar Kebbi, Abubakar Bello Bandam, ya shaida wa wakilinmu cewa, “Makiyayan sun shaida mana cewa an yi musu fashin shanu sama da 2,000 da sanyin safiyar Laraba, aka kora dabbobin zuwa da cikin dajin Zamfara.

“Makiyayan ’yan asalin Jihar Kebbi ne, amma a kauyen Kuchi na Jihar Sakkwato aka tare su, a hanyarsu ta dawowa daga Borgu, Jihar Neja.”

Abubakar Bello Bandam ya ce ganin maharan dauke da muggan makamai ya sa makiyayan tserewa dole domin tsira da rayuwarsu, suka bar dabbobin nasu.

Daga nan su kuma ’yan bindigar suka yi awon gaba da dabbobin gaba daya zuwa maboyarsu da ke dajin Zamfara.

Ya ce an saba a duk shekara a lokacin rani makiyaya kan kai dabbobinsu kiwo a yankin Borgu sannan su juyo da su gida idan damina ta sauka.

Abubakar ya bayyana cewa ba a samu asarar rai ba a harin, amma kawo yanzu ba a samu cikakken labarin halin da makiyayan suke ciki ba.

Amma ya ce yana da kwarin gwiwa cewa jami’an tsaro za su kwato shanun domin tuni an kai wa ’yan sanda rahoto.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, amma abin ya faskara.
Mun kira wayarsa amma babu amsa, kazalika mun tura masa rubutaccen saka, shi ma babu amsa.